zaman takewa
Yajin aikin drebobin taxi a Nijar
An saki sojojin da ake zargi da yunkurin juyin mulki a Nijar
Bayan shafe tsawon watanni takwas a gidan yari a ranar 23 ga watan afrilun wannan shekarar ne wani Alkali ya bayarda belin wasu sojojin da ake tsamanin sun kudri anniyar kifar da Gwamnatin Mouhamadou Issoufou a ranar shaùaya zuwa sha biyu ga watan bakwai na shekarar dubu biyu da sha biyu.
Idan kuna tune zargin da ake yiwa sojojin na yunkurin kiffar da Gwamnatin ya bayyana a cikin wani jawabi ga ‘éan *asa da shugaban kasa Issoufou Mouhamadou yayi a jajibrin ukku ga watan takwas na shekarar bara inda yace wasu sojan sun so su maida hannun agogo baya ‘éan watanni *alilan bayan rantsarda shugaban akan karagar mulki.
Bayan gudanar da bincike akan zargin da ake yiwa sojojin dai alkali ya bayyana sakinsu a 23 ga wannan watan wanda hakan baya rasa nasaba da rashin samun *wa*warar sheda akan zargin da ake yi masu ba.
Manazarta al’amuran yau da kullum na ganin lokaci yayi da yakamata Gwamnati ta fito karara domin bayana sakamakon bincken domin gano baki da farin abubuwan da suka faru a ranar shaùaya zuwa sha biyu ga watan bakwai na shekarar bara.
Ranar 24/ga watan Afrilu Ranar sasantawa da ‘éan tawayen Nijar
Bayan shafe lokaci mai tsawo gwamnatin nijar tana dauki ba dadi da yan tawayen Azbinawan a Arewacin kasar  a ranar 24 ga watan aprilun shekar 1995 ne gwamnatin ta sasantawa da yan tawaye wanda ya sanya yan tawayen suka bayar da makammansu tare da bayar da tabbaacin za su kawo gudun mawarsu a fannoni daban daban domin samun zaman lafiya mai dorewa da kuma ci-gaban Nijar.dauko daga wannan lokacin zuwa yau bangarorin biyu na yan tawaye da na gwamnati na ci gaba da biyayya ga yarjejeniyar da suka ratabawa hannu wanda hakan har ya haifar da karbar makamai da kone su a shekarar 2000 yayin mulkin tsohuwar gwamnatin jamhuriya ta biyar
tun a wannan lokacin ne hukumomi suka saka ranar ashirin da hudu ga Afrilu na kowace shekara a matsayin ranar hadin kan yan kasa.
taken ranar dai a wannan shekara shine kara dankon zumunci domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa kana a wannan shekara hukumomi jamhuriyar Nijar sun zabi gundumar Cintabaraden dake a cikin jihar Tawa domin gudanar da shagugullan tunawa da wannan ranar mai matukar mahimanci ga yan Nijar.
A cikin wata firar da yayi da wannan tashar dan majalisar dokoki ILA OUSMANEÂ shugaban kwamitin tsaro a majalisar dokokin Nijar ya tabbatar da cewar suna duk iya kacin kokarinsu domin ganin sun magance duk wata fitina ko tarzomar da ke iya ta sowa a Nijar
Kana dan majalisar ya kara da cewar babbar gudumuwar da suke kawowa a majalisar ita ce duba ka’idodin da doka ta tanada da kuma kiyaye shari’a saboda baiwa kowane dan kas ayancinsa a fanni doka kamar yanda kundin tsarin mulkin kasa ya tanada….
Â
Gobara a kasuwanni yamai
Duk da kokarin da kasar Nijar keyi ta fannin bunkasar tattalin arziki da ci-gaban kasuwanci, wani abun da ke kan hanyar tauye wannan kokarin shine bala’in gobarar da ake samu akai akai cikin wasu kasuwannin manya manyan birane, Wanda hakan ke haddasa gibi da koma baya kan manufar da kasar ta ke da shi na shiga jerin kasashe masu bunkasar tattalin arzik a afrika.Tarihi ya nuna cewar gobara ta farko mafi muni wace ta yi sanadiyar hasarar dubban miliyoyin cefa ta faru ne a shekarar 1982 wanda hakan ya karya wasu manyan yan kasuwa da dama,haka kuma abin ya sake faruwa da babbar kasuwar shekaru sama da ashirin baya a shekarar 2009 kenan,kaddarar gobarar ta taba rutsawa da kasuwar katako a shekarar 2006,kana a baya bayan nan wata gobarar ta rutsa da wasu kasuwanni 2 kamar kasuwar wadata da kuma da kasuwar yantala,wanda uwa uba wace ta fi daukar hankali itace wata gobrar ta barke a karamar kasuwar birnin yamai a daren hudu zuwa biyar ga watan afrilun wannan shekarar da muke ciki.
Duk wadannn gobarar da aka sha samu dai sunyi sanadiyar hasararr dukiyoyin da basada adadi da kuma zama musababbin talaucin wadansu yan kasuwa.
Ko da yake wani abin mamakin shin a ko da yushe idan irin hakan ta faru gwamnati kan kirkiro da wani kwamiti kumshe da jami’an bincike domin gano makasudin tashin gobarar,to amma kuma wasu lokutta sai kaji shuru wai kamar an shuka dusa akan wayi gari ba tare da an samun sakamakon binciken ba,duk ko da yake suna shirya tarurukan da wasu ke ganin tamkar na shan shayi ne kawai.
Ba shakka dai idan har ana bukatar kawar da matsalolin gobara a kasuwanin to ya zama tilas a yiwa kasuwannin tsari irin na zamani kamar samar da wadatattun hanyoyi a cikin kasuwanni domin samun shigar motocin jami’an kwana-kwana da kuma samarwa jami’an kashe gobara motoci masu karko da inganci saboda kai daukin gaggawa idan har bukatar hakan ta taso.
A nasa bangare shugaban kasa Issoufou Mouhamadou yayi alwashin kawo sauyi da kuma daukar matakan gyara kasuwanni a cikin wani tsarinsa na yamai gnala,sai dai kafin wannan lokacin yan kasuwar Nijar wadanda sukayi hasara da wadanda suka rasa wuraren zamansu a kasuwannin zasu zura wa Allah ido domin neman mafita akan abinda ya faru garesu…..
Gobara a ofishin ministan gidan gona a Nijar
Duk da yake gobarar bata hadasa wata hasara ba wutar tayi gaba da tarnsformer din wuta da ke ofishin .
yaki ya turnike a yayin gobarar to amma jami’an kwana kwana sun gaggauta murkushe wutar
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da wani ofishin minister ke shiga hadarin gobara,idan kuna tune a farko farkon sabuwar shekar nan ma wata gobara ta lakume kusan ilahirin benen farko na ofishin ministan shari’ar Nijar wanda har yanzu ba wani sakamakon da aka bayyana domin hakikance dalilan da suka hadasa gobarar.
Har gobe gwamnati itace da alhakin kare rayuwar al’umma da kuma kyautata ta a ko wane fanni domin haka kundin tsarin mulki ya tanada ya zama dole kenan a dauki matakan kariya domin hana yawan tashe tashen gobara musamanma a ofisoshin gwamnati wanda ba karamar hasara yake janyowa tafiyar ayukan gwamnati bad a ita kanta demokradiyar Nijar



zaman takewa









